An kama Rahama Sadau

Rahotanni na cewa, Jami’an ‘yan sanda sun kama fitacciyar jarumar finafinan Hausa Rahama Sadau a Abuja. Wani babban dan jarida kana tsohon Editan mujallar Fim Aliyu Gora II ya rubuta a shafinsa na Facebook cewaWata majiya da muka samu daga Jaridar MURYAR ƳANCI ta ce an kama jarumar ne tare da mahaifiyar ta da kannen ta, bayan sun kammala shirye-shiryen barin Nijeriya zuwa kasar Dubai.

Idan dai ba a manta ba, Rahama Sadauta ta wallafa wasu hotunan da ke bayyana tsiraicin ta a shafin ta na Twitter, inda Wani masoyin ta ya yi amfani da hoton ya yi batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W.) Lamarin dai ya tada kura a tsakanin al’ummar Musulmi, inda Wani mai rajin kare Hakkin Musulunci Muhammad Lawal Gusau ya rubuta wa shugaban ‘yan sandan Nijeriya korafi.

Biyo bayan umurnin shugaban ‘yan sandan Nijeriya, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna CP U.M Muri ya baza jamin sa, inda su ka bazama farautar Rahama har su ka gano maboyar ta a birnin Abuja.

Lawal Muhammad Gusau dai ya lashi takobin cewa, ko da dukiyar shi za ta kare sai ya tabbatar jarumar ta fuskanci hukunci, domin a cewar sa, ba zai taba lamuntar duk wani mataki na cin zarafin fiyayyen halitta ba matukar ya na numfashi.

Datti Assalafy ne ya Ruwaito a shafinsa na Facebook.