Bayanan Sirrin Boko Haram Da Ya Kamata A Sani.

“..Boko Haram suna sayen kowani litar man fetur daya akan kudi naira dubu hudu (4000)…” ~Datti Assalafiy

Ya kai ‘dan uwa ‘dan Nigeria, ka zauna ka nutsu sosai kayi tunani akan cewa ta wace hanyoyi ne ‘yan Boko Haram suke samun tallafi na man fetur, iskar gas, da sauran kayan masarufi tunda babu rijiyar man fetur a jajin sambisa, tafkin chadi da sauran maboyar ‘yan ta’adda? Duk wanda yayi tunani akan wannan, to zai bawa kansa amsar cewa tabbas akwai hanyar da ake kaiwa wadannan ‘yan ta’adda abubuwan da suke bukata, don haka zargi zai fada kan nau’ukan mutane uku da suke kulla mu’amalar kasuwanci da Boko Haram kamar:

(1) Kungiyoyin da ba na gwamnati ba (NGOs) abin zargi ne, domin rundinar Operation Lafiya Dole ta taba kamasu da laifin tallafawa Boko Haram har ta dakatar da ayyukan NGO din

(2) Mutanen cikin gari fararen hula da suke zaune a kauyuka da birane akwai zargin suna safaran man fetur da kayan abinci zuwa ga ‘yan ta’addan da suke cikin jeji

(3) Jami’an tsaron gwamati suma akwai zargi akan wasun su da suke taimakon Boko Haram da bayanan sirri da wasu abubuwa makamantan hakaWani zaiyi tambaya, ta wace hanya ake bi a isarwa ‘yan Boko Haram da wadannan abubuwa da yake taimakon ta’addancinsu?,

a biyoni har karshen wannan rubutun Mutumin nan da yayi bayan a cikin audio wallahi ban sanshi ba, ban san dalilin da yasa yayi ba, amma na rantse da Allah abinda ya fada gaskiya ne tsantsa a cikinsa, wannan abune da duk wanda yake bincike akan ta’addancin Boko Haram ya sani, sai dai abinda ba zan gaskatashi ba shine zargin da ya yiwa mutanen Zabarmari wadanda Boko Haram suka yiwa yankan rago, bani da tabbaci akan zarginsu da yayi suna huldar kasuwanci da Boko Haram, amma yadda ya fada din nan hakane abinda yake faruwa, mun san mu’alar Boko Haram fiye da duk yadda mutane suke tsammaniJama’a ku sani cewa, tun daga sadda sojojin Nigeria suka fara fada da Boko Haram a jejin sambisa da sahara.

Duk wannan ruwan bama-bamai da ake yi tsakanin sojoji da ‘yan Boko Haram a jeji akwai wadanda su ba ‘yan Boko Haram bane, ba su da wata alaka na kusa ko nesa da akidun Boko Haram sai alaka na bakar kasuwanci da ‘yan Boko Haram din, ba su fasa ba har zuwa yau, ‘yan Nigeria ne, suna nan cikin wannan wutar da ake zubawa a jeji suna buya, haka sukeyi su debi kaya daga cikin Nigeria su shigar dashi jeji su sayar wa Boko Haram Wannan yaron da ya bayyana a faifan bidiyon Boko Haram yana mai daukar alhakkin kisan da kungiyarsu ta Boko Haram suka yiwa mutanen Zabarmari ba wani bane face Ibrahim ‘dan gidan Muhammad Yusuf wanda ya kafa Boko Haram, dansa ne na cikinsa, shine ‘dan Muhammad Yusuf na uku, bayan Yusuf, sai Habib (Albanawiy), sai shi Ibrahim, Yusuf an kashe shi a Kano tun kafin su shiga jeji,

Habib Albarnawiy ya yiwa Shekau tawaye yabi ISWAP har ya zama shugaba, amma shi Ibrahim wanda yayi wannan bidiyon har yau yana raye, yana tare da Shekau a Sambisa da kuma mahaifiyarsa wacce take auren Shekau a yanzu, ba su bi su Albarnawiy ba Tafkin Chadi baJama’a bari na baku wasu point da zaku kula da su, zan saka audion din wani mutum ya fitar wanda Dattawan Borno suka zargi manyan sojoji da tsarawa, da kuma bidiyon da Ibrahim Muhammad Yusuf yayi yana mai daukar alhakkin harin Zabarmari.

Amma satar amsa da zan baku shine, kunga wannan gabashin jihar Borno inda Zabarmari yake, mabiyan Shekau ba su da yawa a yankin mafi yawanci yawo sukeyi a yankin, ba su da wani asalin guri da suke zama, Mobile Operation suke yi, idan ‘yan leken asiri sun gano su anan yau, to gobe ba za’a samu kowa a gurin ba, kuma basa yin nesa da guraren saboda suna yin nisa zasu tarar da mutanen ISWAP su kashe su, mutanen Shekau ba su da yawa sam a gabashin BornoTo jama’a kuyi tunani, abu na farko: yaya akayi ba su da yawa haka suka iya kama kusan mutum 103, ko 70 ko 43 kamar yadda bayanai sukaci karo da juna, ya akayi suka kamasu hanu da hanu suka dauresu suna yankawa kamar raguna? Abu na biyu: Duk mutanen da aka kashe a Zabarmari a kula da yadda salon abin ya faru da kyau, ba wai harbi da bindiga aka yi ba, don haka ku koma ku saurari audio din da Dattawan Borno suke zargin manyan sojoji da tsarawa, da bidiyon da Ibrahim Muhammad Yusuf ya fitar, zaku ji yana cewa ai wadannan da suka yanka sunci amanarsu ne, sun kama ‘dan uwansu suka mikawa sojoji shiyasa suka dauki fansaShi kuma a audio din da Dattawan Borno suka zargi sojoji zaku ji yana cewa a’a ba Boko Haram sun kama mutanen suna bada bayanan sirrin wa sojoji bane, kawai dai Allah ne Ya kawo wani dalili da zai haddasa sabani tsakanin su har suka yiwa mutanen yankan rago, yace abinda ya faru shine su ‘yan Boko Haram din ne suka hango mutanen da kafin su yanka sun hadu da sojoji, sai sukayi tsammanin mutanen ne suka turo sojojin alhali su kuma sun wuce ne kawai abinsuBayan haka, batun cewa mutanen kauyukan nan suna huldar kasuwanci da Boko Haram ba karya bane wallahi, kuma ba karamin kudi suke samu ba a wannan harka na kasuwanci da Boko Haram, Boko Haram suna sayen litar man fetur daya akan kudi naira dubu hudu, litar man fetur din da ake sayarwa 150 a Nigeria, Boko Haram suna saya dubu 4000Sai dai hanyoyin da suke bi su isar da kayan ga ‘yan Boko Haram shima na da matukar wahala, don Allah ku biyo bashin rubutu na musamman da zan wallafa akan hanyoyin da wasu gurbatattun ‘yan Nigeria suke huldar kasuwanci da Boko HaramKafin zuwan wannan gwamnatin, mutanen Zabarmari basa kauyukansu duk sun gudu, wasun su ‘yan Sokoto ne, Katsina da Zamfara amma sun zama ‘yan Zabarmari, duk sun gudu can kan karuwa a Tafkin Chadi suna kama kifi, to zuwan ISWAP suka koro su suka dawo ZabarmariSannan yadda akayi ta zuzuta faruwar abinda ya faru a Zabarmari a kafofin sada zumunta babu abinda su Abubakar Shekau suke kauna yau a duniya kamar su ga ana yada ta’addancin da sukayi a kafofin watsa labarai, duk abinda ya shafi ta’addancin Boko Haram wanda zai zamto ana yayatashi a dukkan kafofin watsa labarai da na sada zumunta to wannan yana burge Shekau.

kuma yana kara masa kaimi, gurin da aka boyeni a kurkukun karkashin kasa a Abuja, na hadu da wani kwamandan yakin Boko Haram da yake tsare a guri wanda ya tabbatar min da hakaJama’a bari na bamu misali da lokacin da Boko Haram suka kama ‘yan matan Chibok, asali fa ba kama ‘yan matan makarantan Chibok ya kaisu garin ba, sunje satar babban janareto na makarantar ne, sai suka ga kawai ba ri suyi riban kafa, sai kwamandan da ya jagorancesu yace a kwashi matan makarantar, da suka tafi dasu jeji sai yaji tsoro kada Shekau yace masa mai yasa ka kwashi matan?, shi kansa Shekau a lokacin bai san me zaiyi da matan Chibok din ba, har yana tunanin sake su, kawai sai yaji labari duk duniya media ta dauka ana cewa Shekau ya sace matan Chibok, an fara kamfen din Free Chibok Girls da Bring Back Our Girls, don haka sai abin ya burge Shekau, ya ga cewa yayi abinda ya girgiza duniya, don haka sai ya rike matanTo kamar misali ne na kawo da abinda ya faru a Zabarmari, duk matsalar tsaro da akace an siyasantar ana ta yayatawa a media to wannan yana karfafa gwiwar ‘yan ta’addan, yana kuma kara musu kaimi akan ayyukansu na ta’addanci, don haka akwai bukatar a yiwa harkokin media a Nigeria garambawul domin media na taimakon Boko Haram sosai, wannan sirrin Boko Haram ne da ya kamata mu sani, sannan ya zama dole gwamnatin Nigeria ta farauci wasu maciya amana ‘yan Nigeria ‘yan jarida da suka fake da aikin jarida suka gudu Kasar Dubai, England wasu suna Nigeria suna taimakon Boko Haram wajen fitar da sakonnin da Boko Haram suke tura musu suna yadawa a media, wanda nake zargin Boko Haram suna biyansu makudan kudiJama’a kar kuyi mamakin Shekau ya sa an kashe abokan huldarsu na kasuwanci, cin amana a gurin Shekau ba sabon abu bane.

Abubakar Shekau har manyan kwamandojin yakinsa irin su Mustapha Chadi, Abu Ibrahim, Kaka Allai, Abu Mujahid, Baba Abdulmalik, Malam Muhammad Auwal Gombe duk ya kashe, to balle kuma wadanda suke taimaka masa ta hanyar kasuwanci? Daga karshe, ina yin addu’a, wadanda basu da hakki a cikin mutanen da Boko Haram suka yanka a Zabarmari Allah Ya gafarta musu, wadanda suke taimakon Boko Haram a cikinsu Allah Ya san yadda zaiyi da suAyi hakuri, tun bayan cin amanar da aka min a 2017 ban cika son fitar da wasu bayanai na sirri akan Boko Haram ba saboda masalaha na ‘yan uwa da abokan arziki, to amma idan an shiga rudani irin wannan na kanso nayi bayani don kar a bar mutane cikin duhuYaa Allah Ka kawomana karshen ta’addancin Boko Haram da masu tallafa musu ta kowace irin hanya Amin

Datti Assalafiy ya Rubuta a faccebook page