Dumi-Dumi: Jami’an Tason Road Safety zasu fara rike Bindiga — Majalisar Tarayya
Rahotanni sun nuna cewa Majalisar Tarayyar Najeriya ta bukaci da a baiwa jami’an tsaron Road Safety damar rike bindiga.
Hakan ya bayyana ne ya yin da kwamitin majalisar ke karbar gabatar da kasafin kudin hukumar na shekarar 2021.
Shugaban Kwamitin, Akinfolarin Mayowa ya bayyana cewa, dokar FRSC ta 1992 ta baiwa jami’an damar rike makamai, kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.
Shin kuna goyon bayan barin jami’an tsaron Road Safety da rike bindiga ?