Wata Sabuwa akan kisan Zabarmari.
Akwai wani sako cikin audio da yake kawo a dandalin WhatsApp akan kisan Zabarmari, wanda sakon ke kokarin nuna cewa wadanda aka yiwa yankan rago maciya amanar tsaron Nigeria ne, wadanda suke taimakon Boko Haram Kungiyar Dattawan Jihar Borno ta mayar da raddi akan audion, inda ta zargi wasu manyan hafsoshin sojin Nigeria da daukar nauyin fitar da audio dinKungiyar Dattawan Jihar Borno sunce ayi watsi da audion, ba gaskiya bane, wasu miyagu ne kawai da suke cin riba da ta’addancin Boko Haram sune suka dauki nauyin tsarawa da fitar da audionMatsayar Datti Assalafiy a takaice:
(1) Ban goyi bayan abinda yake cikin audio din ba
(2) Ban goyi bayan zargin da kungiyar Dattawan jihar Borno suka yi ba
(3) Ban goyi bayan cewa babu wadanda suke taimakon Boko Haram a Zabarmari ba
Jama’a ku biyo Datti Assalafiy bashin wani rubutu da zan wallafa na bincike akan sirrin Boko Haram zuwa daren yau Insha AllahAllah Ka kare mu, Ka taimakemu akan gaskiya Amin